Labaran Duniya

Ana zargin Wata mata da kashe yayan kishiyarta 3 ta hanyar basu shayin aka gauraya da guba

Wani babban al’amari daya faru a garin potiskum dake arewacin najeriya yaja hankulan al’umma da dama.

Ana zargin wata mata da kashe yayan kishiyarta 3 ta hanyar basu shayi wanda aka gauraya da guba bayan sun sha sukace ga garinku nan.

Yaran da ake kyautata zaton sunsha shayin su 4 ne inda tuni 3 daga ciki suka rasu, daya namiji uku mata, inda dayan yaron yake kwance a asibiti yake jinya.

Mahaifin yaran dake zaune a unguwar makara huta dake Potiskum,alhaji haruna ya tabbatarwa da Jaridar BBC hausa da faruwar al’amarin, inda yace yana zargin matarsa da kashe yaransa guda uku, inda tuni yansanda suka kamata.

Mahaifin yaran yace yadauki wannan amatsayin jarrabawa ce daga allah,inda yace kowane bawa da kwai irin jarrabawar da ubangiji yakeyi masa.

“Ina gurin aiki aka kirani akace ana zargin anbawa yayana shayi, kuma ana zargin shayinnan da guba aciki, kuma mukaje asibiti aka bincika aka tabbatar da hakane” inji mahaifin yaran.

“Wanda yayi wannan to tsakaninsa da ubangijinsane, ubangijin daya haliccesu yafini son su, da saninsa da yardarsa aka dauki rayukansu” inji shi.

Mahaifin yaran yakara dacewa koda aka kai wadda ake zargi gaban yan sanda sai tafake dacewa itama bata da lafiya aduba lafiyarta inji BBC HAUSA.

Daga bangaren jami’an tsaron najeriya, ASP Dungus Abdulkharim, shine kakakin yan sanda a jihar yobe yakuma tabbatarwa da BBC HAUSA faruwar al’amarin.

ASP ya bayyana cewa tuni suka kama wacce ake zargin domin bincike kan dalilin dayasa takashe yaran da kuma irin gubar datayi amfani da ita.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button