siyasa

Sanatoci 3, yan majalisu hudu na shiri karbe APC daga hannun ganduje.

A wani rahoto da jaridar DAILY NIGERIAN tafitar ya bayyana cewa da akwai wasu sanatoci 3 dakuma yan majalisu 4 wadanda suka shirya tsaf, domin karbe shugabancin jam’iyar APC a babban taron da za’a gudanar.

Duka sanatocin guda uku, malam ibrahim shekarau (APC kano ta tsakiya) Senator kabiru gaya (APC kano ta kudu) dakuma Barau jibril( APC kano ta arewa) tareda sanatocin sun shirya tsaf domin cika wannan kuduri nasu.

Mambobin, karkashin jagorancin shugaban kwamitin tsaro na majalisar, Sha’aban sharada (APC kano muncipal) sune, Tijjani jobe (APC dawakin-tofa/tofa/ rimingado) Haruna Dederi (APC karaye da rogo) Da kuma Nasiru audu (APC Gabasawa da gezawa).

Sanatocin da mambobin sun hadu jiya talata a asokoro gidan tsohon gwamnan kano, sanata ibrahim shekarau.

Wasu majiyoyi daga cikin gidan sun bayyana DAILY NIGERIAN cewa anyi taron domin yanda sukaga gwamna ganduje ya hada dukiyar jiha da harkokin jam’iyar dan kansa da kuma iyalansa, shiyasa sukayi taron domin ceto jihar dakuma jam’iyar daga hannunsa.

Wata majiya da bataso a bayyana sunanta tace sanatocin da mambobin sun bayyana damuwa kan zargin cin hanci da almubazzaranci dakuma bannatar da dukiyar jama’ar jihar da gwamnan yakeyi.

A cewar majiyar, yan majalisar sun gama duk shirye-shiryen dazasuyi domin karbe ikon jam’iyar daga hannunsa a babban yaron da yake tafe.

Wata majiya ta shaidawa DAILY NIGERIAN cewa a halin yanzu dai ganduje yana fuskantar rikicin siyasa daga bangarori da dama kuma ta ko ina.

sannan kuma akwai jita-jita na cewa tsohon gwamnan jihar kano,senator rabi’u musa kwankwaso, zai’iya komawa jam’iyar.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button