Ganduje yana shirin sawa a kama muhuyi magaji rimin gado A karo na biyu
A wani rahoto da Jaridar DAILY NIGERIAN tafitar ya bayyana cewa saura kiris rundunar yan sandan jihar kano sukama Dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na jihar kano, muhuyi magaji rimin gado, bisa zarginsa da baiwa majalissar jihar kano bayanan karya.
Idan zaku tuna a baya majalissar tanemi muhuyi magaji rimin gado daya bayyana a gabanta ranar 14 ga watan july na shekarar 2021.
Sai dai kuma muhuyi magaji bai amsa gayyatar da majalissar tayi masaba ,illa iyaka dai ya aikewa da majalissar takardun asibiti dasuke nuni dacewa bashi da lafiya a kara masa lokuta domin ya murmure kafin ya masa kirannata.
Sai dai kuma a ranar 19 gawatan, majalissar ta bayyana cewa wadannan takardu daya bayar na bogine.
Bayan majalissa ta tabbatar da bayanan bogi yabayar, Hukumar yan sandan jihar kano suka gayyaci muhuyi magaji domin yazo ya amsa tambayoyi akan tuhumar da ake masa.
- Dalilin da yasa amare basa cin kazar da ango ke kawowa a daren farko
- Wani kare ya mutu har lahira bayan ya shinshini dan kampai
Bayan yan sanda sun tuhumeshi angano cewa bashi da laifin komai inda aka sakeshi sannan aka bashi fasfo dinsa, wanda hakan ke tabbatar da babu wani zargi akansa kamar yanda majiyar jaridar DAILY NIGERIAN ta bayyana mata.
Sai dai kuma wannan hukuncin baiyiwa Gwamnan kano ganduje dadi ba,inda yadage dacewa dole ne a hukunta muhuyi magaji.
Majiyar DAILY NIGERIAN ta bayyana wa jaridad cewa, gwamnan yayi amanna da cewa kama matarsa da hukumar EFCC sukayi muhuyi magaji ne yasa.
Majiyar DAILY NIGERIANTa bayyana mata cewa yanzu duk an kammala wasu shirye-shirye, a koda yaushe Rundunar yan sanda zasu iya gayyatar muhuyi magaji.


One Comment