Wata mata ta zabgawa sajan dan sanda mari acikin caji office .
Wata kotu a jihar legas ta karme wata mata yar shekaru 55 mai suna, maria taiwo bisa zarginta da marin jami’in dan sanda.
Hukumar yan sanda ta gurfanar da mamatar a gaban kotu bisa zarginta da cin mutuncin dan sanda kamar yanda Jaridar Vanguard ta ruwaito.
Mai shigar da kara, karamin sufeton yan sanda, olusegun oke, ya shaidawa kotu cewa matar ta aikata wannan laifine a ranar 31 gawatan agustan 2021 acikin ofishin yan sandan da ake kulle da danta dake unguwar ogba a jihar legas.
Yace cece kuce ne yahadata da daya daga cikin yan sandan me suna, sajan ameh elijah.
Sai dai kuma ita a nata bangaren wacce ake karar, maria taiwo, ta mysanta al’amarin,inda tace sam bata aikata laifin da ake zarginta dashi ba.
Daga karshe dai alkali ya baiwa wacce ake kara damar belin kanta akan kudi naira dubu dari 100,000.
Sannan kuma alkalin yabada umarnin dage shari’ar zuwa rana 3 nuwamba 2021.








