Kannywood
Trending

Anfara caccakar nafisa abdullahi akan bayyana ficewarta daga cikin shirin labarina na arewa 24.

Al’umma da Dama sun fara caccakar Nafisa abdullahi akan bayyana ficewarta datayi daga cikin shirin labarina na arewa 24 mai dogon zango.

Daya daga cikin masu tsokaci a kafar sada zumunta ta facebook,Yusuf Abacha, ya bayyana cewa binciken dayayi yagano cewa akwai bukatar yiwa mutane karin haske akan abunda ke faruwa a cikin shirin na labarina.

shirin Labarina shirine mai dogon zango wanda yayi suna matuka a arewacin najeriya wanda tashar arewa 24 da kuma saira movies suke haskashi a channel dinsu na YouTube.

shirin Labarina ya daga daraja dakuma sunan nafisat abdullahi wacce tafito a rol din sumayya, acikin shirin na labarina.

Darakta aminu saira yayi matukar basira,Saboda lokacin da jarumar ta nuna zata fita daga cikin shirin, sai daraktan yanuna cewa anyi garkuwa da ita domin yasamawa kansa lokaci yasamo mafita,harma yasami mafita domin shirin dayake na canzawa jarumar fuska, bayan ya bayyana cewa harin bomb ya rutsa da jarumar har ya taba fuskarta.

Sai dai kuma a ranar lahadi data gabata jarumar tafito tasanarwa duniya ficewarta daga cikin shirin na labarina, wanda hakan ke nuni da kamar jarumar na kokarin rusa basirar darakta aminu saira ne.

Jarumar ta bayyana cewa itama tanaso tafara wasu fina-finai ne a kamfaninta” wadannan dalilai sune sukasa bazan cigaba da fitowa acikin shirin labarina ba” inji ta.

Sai dai Kuma Al’umma da dama naganin wannan wasika da Jarumar tafitar ba komai bane sai kokarin tozarta fim din,domin dayawan fina-finan hausa, indiya dama na kudancin najeriya zakaga ana canza jaruma ko jarumi in matsala ta faru, amma ba’a taba ganin inda jarumar ko jarumin yafito yayi gardama akan canzasa din da akayi ba,irin wannan wanda Nafisat Abdullahi tafito tayi.

Darakta aminu saira tare da nafisat abdullahi

Akwai fina-finai da dama na kasashen ketare wadanda aka canzawa haruman ciki fuska kamar irinsu,’All the way’ wanda kamfanin shirya fim na kasar rasha ya fitar, akwai ‘Two face’ wanda kamfanin shirya fim na Indiya suka fitar, harma kamfanin algaita dub studio suka fassarashi zuwa FUSKA BIYU.

yanzu dai a halin da ake ciki masu kallo sun zura ido domin ganin matakin da darakta aminu saira zai dauka, sannan kuma wacce jarumar za’asaka ta maye gurbin sumayya?.

Anfara caccakar nafisa abdullahi akan bayyana ficewarta daga cikin shirin labarina na arewa 24.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button