Friday, 03 December, 2021

NIN : Sheikh fantami yakasa gano inda yan ta’adda suke da maboyarsu ta tsarin NIN


Yanzu haka antunkari shekara 1 da gwamnatin tarayya tabada sanarwar rufe layukan wayar duk wadanda basu hada layukansu da lambobin katin dan kasa ba.

Sai dai kuma a wani bincike da shedun gani da ido suka tabbatar ya bayyana cewa har yanzu ba’a samu wata cigaba a game da wannan al’amari ba, yayin da sha’anin ta’addanci ke cigaba da yaduwa musamman ma a arewacin najeriya.

A kwanakin baya lokacin da ministan sadarwa, ALI ISAH FANTAMI, ya gabatar da wannan sanarwa, yan najeriya da dama sunyi farinciki domin suna ganin karshen ta’addancin da ake fama dashi yazo,domin ana ganin kamar ministan yakamo hanyar magance matsalar data addabi kasar.

A lokacin ministan yace,

An haramta bude accounts din banki babu NIN.

  • An haramta katin zabe babu NIN.
  • An haramta biyan kudin rabano da fansho ba NIN.
  • Sannan laifi ne kana ma’aikacin gwamnati baka da NIN.

A wannan lokaci al’ummar najeriya musamman ma na karkara sun shiga wani yanayi, yayinda gurin yin rajistar katin dan kasa yacika ya batse kowa na kokarin mallakar nashi.

A yadda ministan yafada, gwamnatin tarayya ta bullo da wannan tsarin domin kawo karshen ta’addancin dayake faruwa a kasar.

Amma kuma har yanzu babu wani abu daya sauya, saboda bayan anyi wannan rajistar zaben halin da aka shiga ciki shine:

  • An sace dalibai 63 a yawuri dake jihar kebbi.
  • Yan bindiga sun sace dalibai dari 600 a kankara dake jihar katsina.
  • Ansace dalibai talatin da tara a kaduna.
  • A zamfara makarantar jengebe ma ansace dalibai 300.

Da sauran wurare da aka sace dakuma kashe wadansu daliban dama farar hula da sojoji wadanda bazasu kiyastu ba, kuma amma har yanzu tsarin NIN bai tabbatar da cewa ko ankamo yan ta’adda masu garkuwa ba.

A wani Rahoton da jaridarmikiya.

Ya bayyana cewa a 30 ga watan disambar 2020 ne gwamnatin tarayya tabada sanarwa akan kulle layukan wayar duk wanda bai hada NIN da layin wayarsa ba.

Daga baya gwamnatin tayi ta tsawaitawa, kuma a wani bincike yanuna har yanzu akwai layukan dabasu da rajista da NIN.

RAHOTO DAGA JARIDAR MIKIYA

0 comments on “NIN : Sheikh fantami yakasa gano inda yan ta’adda suke da maboyarsu ta tsarin NIN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *