“Ni na shirya yanda za’ayi garkuwa da mahaifina saboda za’a bani tukuicin naira 200,000”.-inji wani matashi
Wani matashi daga kauyen rinjin gora dake karamar hukumar matazu a jihar katsina ya furta cewa shi yataimakawa yan fashi masu garkuwa da mutane da bayanai akan yanda zasu sace mahaifinsa saboda bukatar a bashi ladan naira 200,000.
Matashin mai suna, hamza isah, mai kimanin shekaru 25, yasamu sabani da mahaifinsa mai kimanin shekaru 60,alhaji isah maigora, ya bayyanawa rundunar yan sanda bayan yashiga hannu cewa, ya hada baki da wasu mazauna yankin su biyu domin a sace mahaifin nasa,wanda tuni jami’an yan sanda sun kamo mutanen guda biyu.yanzu haka dai mahaifin nasa alhaji isah maigora yana hannun masu garkuwa da mutane.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar katsina,sufeto isah gambo,yagabatar da wanda ake zargi tareda sauran masu laifin da ake zarginsu tare dashi a gaban manema labarai ranar juma’ar data gabata.
- Dalilin da yasa amare basa cin kazar da ango ke kawowa a daren farko
- Wani kare ya mutu har lahira bayan ya shinshini dan kampai
- Rahma Sadau: Yadda na tsallake rijiya da baya a harin jirgin kasar kaduna
- Kalli yadda samari su ke gudun wata budurwa saboda tsawon ta
Wanda ake zargi ya bayyanawa manema labarai cewa “inada matsala da babana,wannan tasa naje wajen auwal magaji na nemi ya taimakamin da taki,yace ba taki kadai ba, har da kudi zai bani idan har zan taimaka musu su sace mahaifina”.
“Nan take yabani naira 20,000 tareda yimin alkawarin bayan sun sace mahaifina aka basu kudin fansa, zasu bani naira 200,000”.
“Nafada musu cewa zaiyi wahala a sace mahaifina saboda katangar gidanmu nada karfi, amma sukace bakomai suka bani wasu layu kusan kala shida domin binnewa a harabar gidanmu, bayan anyi haja da kwanaki uku suka shigo gidan suka sace mahaifinnawa”.
- “Kwankwasiyya ce muke” sabuwar wakar kosan waka mai zafi.
- “Na kashe mutum biyu” inji wani dan bindiga mai shekaru 14
“Bayan anyi garkuwa da mahaifinnawa sai naji nadama tazo min, nakoma gurin auwalu domin na maida kudin da aka bani , amma sai yayi min barazanar cewa, indai har na kuskura na gayawa wani to rayuwa ta zata shiga cikin hadari.”.
“Lokuta da dama idan suka bani umarni ina shan wahala ba kadan ba, wannan tasa nayi niyyar na fasa kwai kowa yaji abunda ake ciki”.
SP GAMBO ya shaida cewa, babban yayan wanda ake zargi, buhari isah, shine yafara shakku akan kanin nasa bayan anyi garkuwa da mahaifinsu, saboda yaji hamza yana alfahari da cewa kwanannan zaisamu kudade masu yawa.
Hakanne yasa yafadawa yan sanda dasu dub al’amarin, bayan anfara bincike sai aka gano da sa hannunsa akan sace mahaifin nasu, bayan an kamasa ya bayyana cewa wani tsohone a unguwarsu ya rudeshi da kyautar kudi tareda alkawarin bashi wasu muddin aikinsu yayi dai-dai.
Sai dai kuma wanda ake zargi da aika-aikar ya bayyana cewa shi baisan da maganar ba yayin da ake cigaba da bincike, kamar yanda mujallar MIKIYA ta wallafa.








