Kannywood
Trending

Kannywood : Jaruman kannywood 10 wadanda asalinsu ba hausawa bane.

Zamu gabatar muku da jaruman sunayen jaruman kannywood 10 wadanda asalinsu ba hausawa bane.

1) AMINA AMAL :

Hoton jarumar kannywood amina amal ba ba hausawa bace
Amina amal

Jaruma amina amal tana daya daga cikin jaruman kannywood wadanda ba hausawa ba,asalin ta takasancd yar kasar kamaru ce.

Rahotanni sun bayyan cewa jarumar wacce ta fito a fina-finai da dama, lokacin data shigo kasar domin fara harkar fim ko hausa bataji sosai, sai da ta kwashe sama da shekara tana koyon hausa kafin afara sakata a fim.

2) HALIMA ATETE :

Hoton jarumar kannywood halima atete ba hausawa bace
Halima atete

Halima atete ta kasance daya daga cikin jaruman masana’antar kannywood wadanda ale damawa dasu, jarumar ba barbariya ce (barebari) daga jihar borno.

3) MARYAM GIDADO :

Hoton jaruma maryam gidado.
maryam gidado

Itama maryam gidado wacce alafi sani da maryam babban yaro, asalinta ba bahaushiya bace, bafulatatana ce kamar yanda ta fada a wata hira da akayi da ita.

4) SANI DANJA :

Jarumin kannywood sani danja
Sani danja.

Jarumi sani danja yana daya daga cikin manyan jaruman kannywood wadanda suka tsaya tsayin daka domin ganin habakar masana’antar tasu.

Ba kowane zai gane cewa sani danja ba bahaushe bane idan yana magana da hausa, amma kuma asalinsa bayarbe ne.

KARANTA : Fitattun jaruman kannywood 8 wadanda sukafi tashe a shekarar 2021 zuwa yanzu.

5) AINA’U ADE :

Hoton jarumar kannywood aina'u ade
Aina’u ade

Jaruma ai na’u ade tana daya daga cikin jaruman dasuka tsafe tsawon shekaru ana damawa dasu a masana’antar kannywood, itama asalinta Bayarbiya ce.

6) HASSAN GIGGS :

Hassan giggs

Daya daga cikin fitattun daraktocin kannywood, Hassan giggs, shima asalinsa ba bahaushe bane, Bayarbene.

7)UMMEE ZEEZEE :

Jarumar kannywood ummi zeezee daya daga cikin jaruman  kannywood wadanda ba hausawa
ummi zeezee

Tsohuwar jarumar kannywood, ummee zeezee, ta kasance asalinta yar maiduguri ce,iyayenta kuma yan ba hausawa bane, mahaifiyarta kanuri ce, mahaifinta kuma shuwa’arab.

8) MARYAM WAZIRI :

Daya daga cikin jaruman kannywood wadanda ba hausawa ba
jaruma maryam waziri

Jaruma maryam waziri( laila labarina). tana daya daga cikin jaruman dasukayi suna tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021 sakamakon fitowa acikin shirin Labarina datayi, itama kuma asalinta yar garin gombe ce takasance Batangaliya.

9) MANSURAH ISAH :

Tshohuwar daya daga cikin jaruman kannywood wadanda mansura isah bata cikin hausawa
Hoton mansura isah

Mansurah isah tana daya daga cikin tsofaffin jaruman masana’antar kannywood, sannan asalinta bayerabiya ce.

10) RAHMA MK :

Rahama mk daya daga cikin jaruman kannywood wadanda ba hausawa ba
Jaruma rahama mk

Rahma mk wacce take fitowa acikin shirin kwana casa’in wacce akafi sani da matar gwamna bawa mai kada, itama asalinta ba bahaushiya bace bayerabiya ce.

wadannan sune kadan daga cikin jaruman kannywood wadanda suke ba hausawa ba.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button