Labaran Duniya

Kotu ta sallami matar da ake zargi da kashe kishiyarta a kano.

A zaman kotun da akayi jiya juma’a 08/10/2021, babbar kotun jihar kano da ke zaune a bombai tasallami matar da ake zargi da hallaka kishiyarta.

Mai shari’a, justice nasiru saminu kuwa, yasallami matar mai suna hajara da ake zargi da hallaka kishiyarta da sabulu.

Dayake bayani, lauyan dayake kare wacce aje tuhuma,shazali muhammad, ya roki kotu da cewar,tunda dai lauyoyin gwamnati sun gaza kawo kwararan hujjoji to yakamata kotu ta sallami karar,take kuwa alkalin kotun yasallami karar.

Jaridar mikiya ta zanta da lauyan wacce ake tuhuma, inda ya bayyana musu cewa,

Anbawa lauyan gwamnati lokaci domin ya gabatar da hujjojinsa amma yakasa, saboda haka ita wannan kotu taga cewar yakamata tunda babu hujjoji to asallami shari’ar saboda su masu karar sunacan suna shakatawa amma ita wacce ake karar tana nan a tsare” Inji shi.

Itama matar ta bayyanawa manema labarai cewa.

Gaskiya nayi farinciki sossai lokacin danaji cewa kotu ta bada beli na, ma’an zan’iya tafiya gida”

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button