Friday, 03 December, 2021

An maka jaruma hafsat barauniya a kotu bisa cinye wasu makudan kudade datayi


Gidan rediyon Dala fm ya ruwaito cewa, wani kamfani ya maka Jarumar fina-finan hausa, hafsat idris wacce akafi sani da HAFSAT BARAUNIYA Bisa zarginta da cinye wasu makudan kudade.

Kamfanin ya bayyana cewa yabiya jarumar naira miliyan 1 da dubu dari 300 da aka bata domin daukar rawa, amma kuma tasaba alkawari.

TAKAITACCEN TARIHIN RAYUWAR JARUMA UMMI RAHAB

Rahoton yace, jarumar tazo gurin biki har anfara videon, sai kuma ta gudu aka nemeta aka rasa bata dawo ba, wanda hakan yabatawa kamfanin rai.

Yanzu dai kamfani yana rokon kotu tasa jarumar jarumar tabiyasu kudin su kana tabasu naira miliyan 10.

Wannan miliyan 10 dasuka bukata sun bayyanata matsayin diyyar asarar da jarumar tasa sukayi, domin acewarsu sun dakko hayar kayan aiki, dakuma rashin cika alkawarin datayi.

Zuwa yanzu dai ba’aji tabakin jarumar ba, domin batafito ta musanta batun ba sannan kuma bata tabbatar da batun ba.

2 comments on “An maka jaruma hafsat barauniya a kotu bisa cinye wasu makudan kudade datayi

To, dft Allah yadaidaitatsakaninsu, ameen.

Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *