Idan ajali yayi kira : Matashi yarasa ransa sakamakon shiga rijiya domin dakko wayar abokinsa data fada.
Wani matashi dan shekaru 28 mai suna,Abubakar ibrahim wanda akeyiwa lakabi da abba, yayi numfashinsa na karshe a lokacin dayake kokarin dakko wayar abokinsa, usman sufiyanu, data fada wata tsohuwar rijiya.
Lamarin yafaru ranar asabar 6 ga watan october 2021, da misalin karfe 8:00 na safe, a karamar hukumar Dala dake kano, a unguwar kurna layin masallaci.
- Dalilin da yasa amare basa cin kazar da ango ke kawowa a daren farko
- Wani kare ya mutu har lahira bayan ya shinshini dan kampai
A wani rahoto da JOURNAL VIEW HAUSA ta ruwaito ya bayyana cewa, matashin yashiga rijiyar da misalin karfe 8:00 na safe, sai dai kuma shigar sa keda wuya sai aka daina jin duriyarsa.
Lokacin da akayi kokarin kaimasa dauki tuni rai yayi halinsa, daga nan aka dakko gawarsa akayi masa suttura aka kaishi makwancinsa na karshe.
KARANTA : Barayin waya a kano sun hallaka wani matashi mai shekaru 30 a kano.
MUBARAK SANI MUHAMMAD , Wanda shine yafitar da rahoton, ya bayyana cewa yayi kokarin jin tabakin daya daga cikin abokan mamacin mai suna, Aminu saleh, amma hakan ya citura.








