Kannywood
Trending

Fitattun jaruman kannywood 8 wadanda sukafi tashe a shekarar 2021 zuwa yanzu.

Zamu gabatar muku da cikakken bayani akan fitattun jaruman kannywood 8 wadanda sukafi tashe a shekarar 2021/2022 ko kuma muce wadanda tauraruwarsu tafi haskawa a Shekarar.

1. LAWAN AHMAD.

Lawan Ahmad
Jarumi lawan ahmad.

lawan ahmad yana daya daga cikin jaruman hausa na masana’antar kannywood wanda tauraruwarsu tafi haskawa a shekarar 2021,yadade yana fitowa acikin finafinan hausa amma tauraruwarsa bata taba haskawa kamar a shekarar 2021 ba.

Tauraruwar lawan ahmad tafara tashe ne alokacin da yafara fitowa acikin shirin izzar so,wanda suke fitarwa a YouTube Channel dinsu ta bakori TV. Shirin izzarso yayi tasiri matuka gurin samun daukakar wasu jarumai na masana’antar kannywood, ciki harda shi kansa lawan ahmad din.

2. Adam abdullahi adam (ABALE OJO).

Daddy hikima/Abale ojo
DADDY HIKIMA

Ga dukkan alamu zamu’iya cewa Abale ojo ko kuma daddy hikima ya shigo masana’antar kannywood da kafar dama, domin kuwa a watannin dayayi yana fim a masana’antar kannywood. yanzu haka dai yana daya daga cikin wadanda tauraruwarsu take haskawa a kannywood.

ya kasance kafin yashigo masana’antar kannywood ma’aikacin asibiti ne.Tauraruwarsa ta fara haska acikin shirin fim din hausa na A duniya,wanda ake gabatarwa a tashar zinariya Tv dake YouTube.

3.Azima gidan Badamasi.

Azima gidan Badamasi.

Jaruma hauwa ayawa tana daya daga cikin jaruman da sukayi tashe a shekarar nan acikin masana’antar kannywood. Biyo bayan shirin da jarumsr tafito mai dogon zango na GIDAN BADAMASI wanda ake gabatarwa a tashar Arewa 24 dakuma Dorayi film PRODUCTION dake YouTube.

4. Ummi rahab.

Jaruma ummi rahab
Ummi rahab.

Jaruma UMMI RAHAB ta kasance daya daga cikin jaruman kannywood wanda tauraruwarsu ta haska a shekarar 2021 zuwa shekarar 2022, domin jarumar tafito a fina-finai da dama wadanda suka hada,farin wata, wuff ,lamba da dai sauransu.

5.Aisha najamu (Aisha izzar so).

Aisha najamu izzarso fitacciyar jarumar shekarar 2021 zuwa 2022
Aisha najamu izzarso

Aisha najamu itama tauraruwar ta ba ksramin haskawa tayi ba ashekarar nan,biyo bayan fitowarta a shiri mai dogon zango na Izzarso.Kafin wannan lokacin Jarumar ta kasance tana daya daga cikin mawakan siyasa, tana bin mawaka irinsu,tijjani gandu,aminu dumbulun da dai sauransu.

6. NUHU ABDULLAHI.

Nuhu abdullahi daya daga cikin fitattun jaruman kannywood

Jarumi nuhu abdullahi yana daya daga cikin jaruman kannywood da sukayi fice a wannan shekarar,bayan samun nasara ya fito acikin taurarin shirin fim din hausa mai dogon zango na LABARINA.

U.Rabiu Rikadawa.

Rabiu Rikadawa daya daga cikin fitattun jaruman kannywood a shekarar 2021
Rabiu Rikadawa.

Rabiu Rikadawa ko kuma kace Baba dan audu acikin shirin labarina yana daya daga cikin wadanda suke haska shirin labarina,kuma shima shirin yake haskasa.

duk wanda yake kallon shirin labarina tabbas yasan rawar da baba dan audu yake takawa ba karama bace,domin shima kansa tauraro ne.

8. Nafisat abdullahi.

Nafisat abdullahi daya daga cikin jaruman kannywood a shekarar 2021

Jaruma Nafisa Abdullahi ta dade tana shirya fim a kannywood kuma tana fitowa acikin fim,sannan tana daya daga cikin tsofaffin jaruman kannywood,wanda hakan yasa aka santa sossai.

sai dai a Shekarar 2021/2022 tayi tashe matuka kuma tauraruwarta ta kara haskawa acikin shirin labarina.

Wadannan sune jerin sunayen fitattun jaruman kannywood 8 wadanda sukafi tashe a shrmekarar 2021 zuwa 2022.

kuci gaba da kasancewa damu domin samun wasu shriye-shiryen namu masu kayatarwa da zarar mundora.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button