Asirin nuhu abdullahi ya tonu yan kauyensu sun fito sun fadi gaskiya akansa.
Zuwaga jarumi nuhu abdullahi (mahmud acikin shirin Labarina)
Wannan sako yafito daga ishak usman wali, mun dakko shi daga NAIJA FAMILY .
Rubutun yafara da” nayi matukar mamaki irin yanda na kalli hirarka da BBC HAUSA a shirinsu na daga bakin mai ita inda sukaso suji tarihinka.
Kai kuma sai kanuna musu cewa anhaifeka a garin kano sannan kuma kayi primary da secondary duk acikin kano. Hakan baiyimun dadi ba sakamakon ganin yanda ka juyawa kauyenku baya saboda yanzu rayuwarka taci gaba, tabbas nayi mamaki matuka.
- Dalilin da yasa amare basa cin kazar da ango ke kawowa a daren farko
- Wani kare ya mutu har lahira bayan ya shinshini dan kampai
Inason duk wadanda suka kalli hirar su san cewa an haifi nuhu abdullahi a wani kauye mai suna tudun bichi a karamar hukumar danko wassagu dake jihar kebbi,yayi model primary anan tudun bichi.
Daga bayane ya zarce garin wasagu, inda acan yayi makarantar secondary mai suna government arabic and islamic secondary school wasagu, a lokacin marigayi malam ja’afaru ne principal, shikuma malam abubakar nadiri yake mataimaki.
A lokacin nuhu abdullahi shine captain a wasagu house, shikuma abokinsa yake house captain a sakaba.nuhu yasanni kuma nima nasanshi,domin ta sanadiyyar kaninsa aliyu abdullahi muka hadu,sanna mun kwana daki daya dashi (nuhu abdullahin?
A lokacin da ina sabon shiga a makarantar, akwai wani kanin matar yayana frifet mai suna,tijjani garba, ta sanadinsa ne nafara kwana a firifet room(dakin dasu nuhu abdullahi suke) duk da ba house dina bane, domin a lokacin ni ina danko house ne, wanda nura yake jagoranta.
Nuhu abdullahi yasha aikena nadebo masa ruwa a bokiti udan yanaso yabiya bukatu kamr su wanki, wanka da dai sauransu, sakamakon nine junior a dakin kwanannamu.
Lokacin da ake shirin ginin masallaci, alokacin kuma sai nuhu abdullahi yasamu sabanin fahimta da vice principal din makarantar, wato malam abubakar na diri, wanda hakan ne yayi sanadiyyar barinsa daga makarantar, lokacin kuma yana gab da rubuta jarabawarsa ta waec.
Bayan barinsa daga makaranta sai ya tafi gurin yayansa Abdulrahman dake legas, wannan yayan nasa ne sanadiyyar shigarsa cikin harkar fina-finai, kuma acan allah ya taimakeshi yacigaba da karatu har ya kammala jami’a.
Duk rintsi da irin ni’imar dakake ciki bai kamata kacire sunan mahaifarka daga cikin tarihin rayuwarka ba, domin ko ba komai wadannan yan’uwannaka sune kullum sukeyi maka addu’a da fatan alkhairi, sannan kuma suke alfahari dacewa dan’uwansu yasamu daukaka.
Allah yabaka ikon sanin hakkin mahaifarka”.









One Comment