Kannywood

Dalilin da ya sa ake zargin Rahma Sadau da madigo

Dalilin da ya sa ake zargin Rahma Sadau da madigo:

An dade ana dora zargi kala daban-daban ga jaruman masana’antar kannywood musamman ma zakakurin cikin su. A nan kuma mun kawo muku bidiyon dalilin da ya sa ake zargin Rahma Sadau da madigo.

Dalilin kiran Rahma Sadau yar madigo

Duk da Ubangiji ya horewa mata salo daban-daban na yin kwalliya domin su burge maza, amma duk da haka sai su ka karkasa kwalliyar dai dai da halaye ma banbanta daga matan.

A duk lokacin da aka ga mace ta sha foda da jambaki ta sha hijabi sai a yi mata zaton kasancewa mutuniyar kirki. Idan kuwa aka ganta da wasu matsattsun kaya sai gyale sai a fara tunanin yar duniya ce. To amma kuma idan an ganta da wata shiga kamar sanya riga mai santsi ba rigar nono ko kuma sanya sarka a kafa sai a fara zargin ta da kasancewa yar madigo.

A nan mutane da dama sukan zargi Rahma Sadau da kasancewa yar madigo saboda sarkar da ta ke sanya wa a kafarta a duk lokacin da za ta yi hotunan da ta ke sakawa a kafafen sada zumunta. Duk da cewa an yi surutai da yawa a gareta bisa wannan zargi da ake mata amma bata daina saka sarka a kafarta ba.

Kamar yadda ake cewa idan kana son kubuta daga zargin mutane to ka bisani abinda zai sa mutanen su zarge ka, kenan ya kamata Rahma Sadau ta nisanci sanya sarka a kafarta ko dan korewa kanta zargin madigo. To amma sai gashi bisa mamaki kara janye bujenta ma ta ke yi tare da dago kafarta sama a duk lokacin da za ta yi hotunan da za ta sanya a Social media

Dalilin da ya sa ake zargin Rahma Sadau da madigo

Kamar dai yadda mu ka gani a hoton da ke sama, Rahma Sadau tana kokarin nuna sarkar da ke kafarta a cikin hoton, domin kuwa har hannu ta sanya ta dan janye doguwar rigarta domin sarkar ta kara fitowa.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button