Labaran Duniya

Rahoton kwamitin bincike yagano cewa tabbas akwai mu’amala ta sadarwa tsakanin Abba kyari da hushpuppi

Babban sifetan janar na yan sandan najeriya, Usman alkali baba, Ya tuhumi Tsohon kwamandan rundunar IRT, Abba kyari kan alakar dake tsakaninsa da rikakken dan damfarar yanar gizo,ramon abbas, wanda akafi sani da HUSHPUPPI.

Jaridar Legit.ng hausa ta ruwaito cewa ofishin antony janar na tarayya na bukatar a duba bukatar amurka na mika mata fitaccen dan sandan domin bincike.

A ranar lahadi ne jaridar Daily trust ta gano cewa an mika tuhumar ne bayan binciken da wata kwamiti ta gabatar, wacce tagano asalin abubuwan dake faruwa.

Legit.ng hausa ta gano cewa hukumar kula da al’amuran yan sanda ta dakatar da abba kyari daga matsayinsa sakamakon bukatar da alkali ya mika.

Angano cewa kwamitin binciken daya samu shugabancin DIG joseph egbunike, wanda yamika rahoton bincikensa a watan agusta,ya tabbatar da cewa lallai ansamu sadarwa tsakanin abba kyari dakuma dan damfara hushpuppi.

Yace sai dai kwamitin bai bada shawarar mika abba kyari ga kasar amurka ba domin ba’aga wani laifi da dan sandan yayiwa amurka ba.

“Babu wata shaida da ta tabbatar dacewa dan sandan yayiwa kasar amurka laifin daya dace amikashi kasar,hukumomin dasuka dace ne zasu ladaftar dashi”

Sai dai kuma AGF zai bada bukatar ko za’amika shi amurka, wanda dawuya hakan yafaru” Inji shi kamar yanda rahoton Legit.ng hausa ya bayyana.

Kakakin rundunar yansanda, frank mba a wata tattaunawa dayayi a waya,yace kamar yanda aikin dan sanda yake, sifeto janar yamika shawar kwamitin bincike zuwa ga hukumar kula da ayyukan yan sanda domin daukar matakin daya dace.

 

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button