Kannywood

Angano wasu finafinan hausa na kannywood guda 10 wadanda akayi iskanci acikinsu.

Masu shirya finafinan hausa sun fara saka batsa acikin fina-finai masu dogon zango.

Wani dan jarida mai bincike akan FINAFINAN HAUSA,Yusuf Abacha, ya gano wasu finafinan hausa guda 10 wadanda wadanda aka sako batsa aciki.Harma daga cikin guda goman yayi fashin baki akan guda daya.

Akwai wani shotin fim din hausa mai suna’Shakundum‘, wanda kamfanin sultan film factory suka shirya, acikin fim din Episode 10 daidai mintuna 20, annuno jarumi yamu baba, wanda akafi sani da angon sambisa yana cire wandonsa.Wanda hakan yasabawa tsarin addini, kamar yanda AREWA MEDIA ta ruwaito.

Jarumin kannywood yamu baba

“Yan fim wadanda akafi sani da yan drama, suna daga cikin yan kungiyoyin boko Akida mafi hatsariga Al’umma, kuma mafi tasiri a kanta.Saboda Sune suke yada Barnarsu a Aikace, kuma a cikin jama’a,batare da wani tsaiko ko tsangwama ba”. Inji yusuf

Ya kara da cewa”Duka kungiyoyin boko akida kusan sunyi tarayya gurin hallata alfasha dakuma yaki da addinai kyawawa da dabiu,inda dukkansu kusan sun dauki wannan a matsayin babbar manufa, kuma jigo a tafiyar su.

kungiyoyin boko akida tun daga kan masuniya(freemasonry, Masonic) da sakulanci (secularism),da gurguzanci (socialism),da kwaminisanci (communism),ilhadi (Atheism).Duka wadannan kungiyoyi da hanyoyi na tsarin rayuwa,duka sunyi tarayya wajan jefar da addinai acikin rayuwa, dakuma jefar da kyawawan halaye da dabi’u,bisa ikirarin yancin rayuwa.

To su wadannan yan fim,an samar dasu ne domin yada akidar yancin rayuwa batare da zama karkashin kaidin addini ko kyawawan dabiu na kunya da kamun kai batare da yakinsu ba.

Shiyasa za’aga finafinai da ake duja kusan suna kirane da bayyana tsaraici da kuma yaduwar alfasha cikin al’umma ta hanyar cire shamaki tsakanin jinsin maza da mata.

shiyasa kaga yan fim sun zama hanya mafi muhimmanci ga yan kungiyar boko akida, wajen watsa barna da sharri acikin al’umma.

Ya karkare rubutunsa da cewa”A kasar turai, Akwai wata kungiya ta boko akida datayi fice akan wannan manufa ta yada alfasha dakuma yaki da kyawawan dabiu (libertine), wacce ake kira da wayewa(modernity),wadanda suja tattaro tunaninsu da akidunsu daga wasu munanan kungiyoyi masu yawa,kamar Marxism, freudian da sauransu.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button