Duniya ina zaki damu : Dan shekara 34 yayiwa diyar Abokinsa mai shekaru 10 fyade.
Rundunar YAN SANDAN jihar legas, ta cafke wani mutum mai suna,Godwin iroro,mai kimanin shekaru 34 bisa zargin yiwa yar abokinsa mai shekaru 10 fyade.
Jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA ta wallafa cewa kakakin rundunar yan sandan, adekunle ajisebutu shine ya bayyana haka a wata sanarwa daya fitar a ranar asabar 27 ga watan NOVEMBER 2021.
Adekunle yace ancafke iroro ne a ranar 25 ga watan November bayan da mahaifin yarinyar, chukudi chime,yakai korafi a shedikwatar yan sanda dake ajegunle.yace yalura da wani yanayi da yar tasa tashiga shiyasa yabincika kuma ya tabbatar anyi mata Fyade.
“Lokacin da ake tambayar yarinyar akan wanda yayi mata haka, sai ta kada baki tace abokin mahaifinnata,wanda yake da yaya hudu kuma suke zaune a gida daya mai lamba 5, layin iyalode ajegunle a Legas ya mata fyaden a lokacin da mahaifinta baya nan”inji kakakin.

Kakakin yakara dacewa ” binciken farko ya tabbatar dacewa duka mazan biyu basa tareda matansu,bayan da yarinyar take tareda mahaifinta a adireshin sama,shikuma mai laifin matarsa tana jihar asaba a delta tareda yayansa hudu”.
Yace bayan da aka tuhumeshi, iroro ya amsa laifinsa amma kuma yadora laifin akan shedan.
Kamfanin dillancin labarai na NAN, ya ruwaito cewa, kakakin yakuma ce mai maifin ya bayyana cewa yayiwa yarinyar fyade sau biyu kafin dubunsa tacika.
Kakakin ya bayyana cewa kwamishinan yan sandan jihar, Hakeem Odumosu ransa ya baci da lamarin,inda ya umarci da akai mai laifin sashin kula da jinsi na shedikwatar domin bincike dakuma hukunci.
Zaku iya ajiye mana ra’ayinku a akwatin comments dayake kasa domin bayyana mana ra’ayoyinku.









One Comment