Abun takaici : Tsoho mai shekaru 70 yayiwa yarinya yar shekara 7 fyade.
Jami’an yan sanda shiyya ta 12 a jihar bauchi, sun kama wani tsoho mai kimanin shekaru 70 da laifin yiwa yarinya yarshekara 7 fyade.
Tsohon da aka bayyana sunansa da alhaji umaru daura, ana zarginsa da aikata fyade ga yar makocinsa yar shekara 7.
Hakan na kunshe a cikin wata takardar sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan shiyyar, SP thomas goni,wanda aka rabawa manema labarai kwafi a jihar ta bauchi.
KALLI : VIDEO : MUSABBABI HAUSA FILM DAGA KAMFANIN DORAYI FILM PRODUCTION.
A wani rahoto da jaridar KATSINA ONLINE ta wallafa ya bayyana cewa sanarwar tace lamarib yafaru kwanannan a kauyen kawo rauta a jihar bauchi.
SP thomas yacigaba dacewa mahaifin wacce akaiwa fyaden yakai rahoton lamarin zuwa ga yan sanda yana mai cewa” an kama wanda ake zargi dumu-dumu yana lalata diyata yar shekaru 7.
KARANTA : Barayin waya a kano sun hallaka wani matashi mai shekaru 30 a kano.
Ya kara dacewa mataimakin babban sufeton yan sanda Mai kula da shiyya ta 12 a bauchi, AIG AUDU A MADAKI, ya bayar da umarnin gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.









6 Comments