Labaran Duniya

Duniya ina zaki damu : Matashi ya halaka dan’uwansa da wuka.

Wani matashi a jihar rivers ya halaka dan’uwansa da wuka har lahira saboda takaddama tashiga tsakaninsu.

Jaridar DIMOKURADIYYA ta wallafa cewa mutumin mai suna Bobby gabriel mai kimanin shekaru ashirin da doriya , ya halaka dan’uwansa mai suna kopapa nite, wanda shekarunsa sunkai arba’in, yayin da wata takaddama ta barke a tsakaninsu a daren lahadi.

Jaridar ta ruwaito cewa annemi wanda ake zargi da aikata kisan anrasa, wanda hakan yake tabbatar da cewa ya tsere daga garin.

Shugaban kwamitin cigaban al’umma na yankin duburo, vincent gbosi, ya tabbatar da faruwar al’amarin ta wayar salula, sannan ya baygana cewa an kai rahoton ga hedikwatar yan sanda dake yankin bori a jihar rivers.

Mista vincent gbosi ya bayyanawa manema labarai cewa”ajiya akwai wani abu dayafaru a jihar nan,wani mutum ya cakawa dan’uwansa mai shekaru 40 wuka inda mutumin yarasu nan take”.

Sai dai kuma jaridar DIMOKURADIYYA ta bayyana cewa har yazuwa wannan lokacin rundunar yan sandan jihar basu tabbatar da faruwar al’amarin ba.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button