Kotu ta sallami matar da ake zargi da kashe kishiyarta a kano.
A zaman kotun da akayi jiya juma’a 08/10/2021, babbar kotun jihar kano da ke zaune a bombai tasallami matar da ake zargi da hallaka kishiyarta.
Mai shari’a, justice nasiru saminu kuwa, yasallami matar mai suna hajara da ake zargi da hallaka kishiyarta da sabulu.
- Dalilin da yasa amare basa cin kazar da ango ke kawowa a daren farko
- Wani kare ya mutu har lahira bayan ya shinshini dan kampai
Dayake bayani, lauyan dayake kare wacce aje tuhuma,shazali muhammad, ya roki kotu da cewar,tunda dai lauyoyin gwamnati sun gaza kawo kwararan hujjoji to yakamata kotu ta sallami karar,take kuwa alkalin kotun yasallami karar.
Jaridar mikiya ta zanta da lauyan wacce ake tuhuma, inda ya bayyana musu cewa,
“Anbawa lauyan gwamnati lokaci domin ya gabatar da hujjojinsa amma yakasa, saboda haka ita wannan kotu taga cewar yakamata tunda babu hujjoji to asallami shari’ar saboda su masu karar sunacan suna shakatawa amma ita wacce ake karar tana nan a tsare” Inji shi.
- Zargin madigo: Asirin rahma sadau da fati washa ya tonu
- Zan kashe kaina idan har ba’a raba aurena da matata ba-inji wani magidanci.
Itama matar ta bayyanawa manema labarai cewa.
Gaskiya nayi farinciki sossai lokacin danaji cewa kotu ta bada beli na, ma’an zan’iya tafiya gida”








