Yanda Yayana da mijin yayata dakuma kuma yayan mijin yayata su uku sukayi min fyade.
Wata baiwar allah maisuna Aisha, ta bayyana kungiyar RIGAR YANCI INTERNATIONAL, yanda yan uwanta dakuma wasu danginsu sukayi mata fyade.
Acikin wani bidiyo wanda muka ajiye muku a kasan wannan rubutu zakuji yanda Aisha ta bayyana yanda mijin yayarta da yayanta, dakuma yayan mijin yayarta sukayi mata fyade a lokuta daban-daban.
Aisha tace mijin yayarta ne yafara yi mata fyade, ta bayyana cewa duk lokacin da yayarta batanan sai mijinnata yakirata, sannan yahanata fita, kuma ya gargadeta kada tasake tafadawa kowa abunda ke faruwa, sai yabata naira 100.
Budurwar aisha ta bayyana cewa tundaga wannan lokacin Mutumin mai suna Ibrahim yasamu hanyar yi mata fyade.
Daga nan kuma sai ta bayyana yanda yayanta mai suna bala shima yayi lalata da ita ta hanyar fyade, ta bayyana cewa idan zatashiga gida daga waje sai yahanata har sai yayi lalatar da ita, shikuma naira 200 yake bata yayi lalata da ita.
Daganan kuma sai mutum na uku wanda ta bayyana sunansa da ummaru, wanda shine yayan mijin yayarta,shikuma gidansa yake kiranta sannan yabata naira 100 yayi lalata da ita.
Daga nan kuma sai saurayinta, wanda ta bayyana da sunan mijinta,shikuma hakan yana faruwane aduk lokacin dasuka gama fira zata tafi gida, a maimakon hanyar gida sai ya canza mata hanya, idan tabi hanyar daya canza mata sai yayi mata fyade kafin takai gida.
Lokacin datayi aure da wata biyar sai akaje aka aunata kuma akaganta dauke da cikin wata shida, wannan ne yasauwar mijinta tace tatafi gida, shimakuma mijin dayazo sai yakorata gidansu.
Daga baya sai ta haihu, inda yanzu haka mijinnata yaki karbar dan a matsayin nasa, domin a lokacin da abun yafaru ankaisu ofishin yan sanda, amma kwana 2 dayin haka aka sakosu.
Yanzu haka dai case ankai karar gaban kungiyar rigar yanci domin tabiwa yarinyar hakkinta.
Ga videon nan akasa ku kalla domin kusan cikakken abunda yafaru.
Idan kunada sharhi akan wannan video zaku’iya ajiyemana acikin akwatin comment.









One Comment