Wata sabuwa: malaman kano sunyi watsi da tsige malam ibrahim khalil da wasu mutane sukayi.
A wata Takardar sanarwa da jagororin zauren hadin kan malamai da kungiyoyi na addinin musuluci suka fitar, sun nisanta kansu daga juyin mulkin da wasu malamai a jihar kano sukayiwa shaikh ibrahim khalil.
Gamayyar kungiyar tace taji sanarwar abunda wasu mutane a jihar kano suna masu ikirarin cire sheikh ibrahim khalil daga mukaminsa na shugabancin majalisar malamai ta kasa reshen jihar kano, tareda ayyana wanda suke sha’awar ya shugabanceta.
Jagororin sun tabbatar da cewa bada hannunsu akayi wannan jawabi ba kuma basa goyon bayansa.
Jagororin sun bayyan cewa a har kullum suna neman zaman lafiya da Hadin kan al’umma ne, amma kuma wannan abu da wasu mutane suka aikata akano zai haifar da sabani.
Don haka sukai kira da al’umma dasu cigaba da ririta zaman lafiyarsu kuma suguji duk wani abu dazai iya zama barazana ga tsaro da kwanciyar hankali.
Jagororin dasuka amince afitar da sanarwar sun hada da;
- Sheikh abdulwahab abdallah.
- Khalifa Sheikh karibullah sheikh nasir kabara.
- Farfesa musa muhammad borodo.
- Sheikh ibrahim shehu mai hula.
- Farfesa babangida muhammad.
- Dr bashir aliyu umar.
- Imam nasir muhammad adam.
- Dr ibrahim muazzam mai bushara.









