Wata budurwa Ta mutu ana sauran kwana 3 bikinta.
A tsakanin Talata zuwa juma’ar wannan satin babu labarin dayaja Hankalin Al’umma a kafafen sada zumunta, musamman ma na facebook fiye da mutuwar wannan baiwar allah.
Baiwar allahr mai suna Wasilat Attahir, ta masa kiran mahaliccinta ana saura kwana 3 Ayi bikinta.
Wata kawarta marigayiyar ce mai suna, Xahreert Uthman Faruq ta wallafa hotunan amaryar da kuma na katin gayyatar daurin auren amaryar tana mai alhinin rasuwar kawartata.
- Dalilin da yasa amare basa cin kazar da ango ke kawowa a daren farko
- Wani kare ya mutu har lahira bayan ya shinshini dan kampai
Acikin post din data fitar jiya al-hamis ,mhiz Xheert uthman faruq, ta bayyana cewa saura kwana uku bikin marigayiyar kafin mahallicinta ya karbi abarsa.

Acikin post din ta bayyana irin wayar dasukayi da Marigayiyar, inda marigayiyar take tambayarta tazo da ameera ita kuma tace basuyi akawari ba, suna dai raha irinta kawaye.
Ta bayyana cewa wannan shine maganar su ta karshe da marigayiyar sai dai kuma labarin Rasuwarta taji.
Muna Addu’ar allab yaji kanta ya gafarta mata idantamu tazo allah yasa mucika da imani.









Amin Ya Rabbi