Saturday, 25 September, 2021

Ads Banner

Naziru sarkin waka yasa kyautar 1million ga duk wanda yasan inda wadanda suke wata aika aika suke


Sarkin wakar tsohon sarkin kano,naziru m ahmad wanda akafi sani da sarkin waka, ya fito yayi magana akan wani abu dake cimai tuwo a kwarya.

Acikin videon daya fitar mai tsayin minti 9 da doriya, nazir m ahmad yace akwai wani abu da wasu makiya sukeyi wanda yake bata masa rai.

Sarkin waka yace akwai wasu mutane dasuke bin masoyansa ta whatsapp suna tambayarsu kudi, ko kuma suce matarsa bata da lafiya dan allah a taimaka ana bukatar kudi.

Sai su yaudari mutum da sunan sarkin waka su amshi kudin hannunsa ko kuma wani abu daya mallaka, naziru m ahmad ya bayyana cewa wannan abu bayamasa dadi.

A dalilin hakanne naziru m ahmad yakeso a hada hannu da hannu domin kama wadannan bata gari, kuma yayi alkawarin duk wanda ya sansu kuma yabayyanasu to yanada kyautar zunzurutun kudi naira miliyan guda (1million).

Saboda hakane muke sanarda yan uwa dasu taimaka idan sunsan inda wadannan batagari suke suyi magana su samu lada biyu, na kudi dakuma na taimakon al’umma gurin kama bata gari.

Ga duk wanda keson sauraron videon sai yaje YouTube channel dinmu mai suna AREWA STAR TV domin yamore kallo kyauta.

Kada kuma kumanta kudanna jan maballinnan mai suna subscribe sannan kudanna kararrawar sanarwa.

Mungode

0 comments on “Naziru sarkin waka yasa kyautar 1million ga duk wanda yasan inda wadanda suke wata aika aika suke

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *