Mijina yana barazanar kashe ni da yayana
Wata mata ma’aikaciyar gwamnati a abuja mai suna,blessed nwa, tanemi kotu data raba aurenta da mijinta mai suna,ahamefula,saboda yana barazanar kasheta ita da yayanta.
A wani rahoto da jaridar VANGUARD ta ruwaito ya bayyana cewa, a karar da matar tashigar ta bayyana cewa tanaso a raba aurennata wanda yakai shekara biyu saboda barazanar kisa da mijin nata yake mata.
“Mijina ya mun barazar kasheni kuma ba’abunda za’ayi masa, amma nakai kara gurin jami’an yan sanda da kuma hukumar yaki da safarar mutane”. Inji ta.
Matar tace mijinnata bashi da saukin sha’ani, dazarar sun samu sabani sai yakamata da duka.
Sannan tace mijin nata yayi mata barazanar cewa zai sace yayansu yakaisu inda bazata sake ganinsu ba.
A bangaren wanda ake kara,ahamefula, ya musanta duk zargin da matar take masa, ya kuma roki kotu akan kada ta raba aurensu.
Daga karshe dai alkalin kotun ya umarci ma’auratan dasuyi kokarin sasanta kansu,sannan ya dage shari’ar zuwa 1 gawatan disamba 2021









2 Comments