Malamin addinin musulunci yayi garkuwa da Dan’uwansa yanemi a biyasa kudin fansa.
Wani malamin addinin musulunci mazaunin garin katsina yashiga hannun yan sanda bisa zarfinsa da garkuwa da dan’uwansa.
Jami’an tsaro reshen jihar katsina ne suka cafke malamin mai suna,jamilu idris, bisa zargin sace dan’uwansa dan shekara hudu, umar farouq kabir.
KARANTA : Kishi : Budurwa ta cakawa saurayinta wuka bayan ta duba whatsapp dinsa.
A wani rahoto da jaridar THIS DAY ta fitar ya bayyana cewa, malamin mai shekaru 39 ya fito ne daga sabon fegi kauyen yankara karamar hukumar faskari ya sace yaronne tun 9 gawatan October.
Malamin wanda aka gano yanada dalibai 41 wadanda suke koyon karatun alkur’ani mai girma a wurinsa, ya sace yaron bayan daya jawoshi.
Kakakin rundunar yan sandan jihar katsina,gambo isah, ya bayyana wanda ake zargi tareda wasu mutane 13 masu laifuka daban-daban,inda yace malam yanemi abiyashi kudin fansa N5M (NAIRA MILIYAN 5).
“A ranar 25 ga watan October misalin karfe 11:00 na safe aka kama wani jamilu idris mai shekaru 39 daga kauyen yankara”. Inji shi.
“A yayin bincike wanda ake zargi ya amsa laifunsa, sannan ya bayyana yanda ya ziyarci gidan kawunsa a funtua, sannan yayi amfani da lemo waje sace yaron”.
KARANTA : Abun takaici : Tsoho mai shekaru 70 yayiwa yarinya yar shekara 7 fyade.









2 Comments