Saturday, 25 September, 2021

Ads Banner

WATA SABUWA: Kotu ce Zata Rabani da Muaz magaji – kabiru gombe


Fitaccen malamin Addinin muslunci na kungiyar izala,sheikh kabiru gombe, yayi allah wadai da abunda muaz magaji dansarauniya yayi masa na kage da kazafi.

Kamar yanda malamin yafada dai yace yayi allah wadai da kalaman da shi muaz dan sarauniya yayi nacewa sheikh kabiru gombe yakira gwamna mai mala buni na jam’iyar APC yagayamasa cewa muddin idan kwankwaso yakoma jam’iyar APC daga PDP to tabbas zasu bar jam’iyar.

Sheikh kabiru gombe yace”Muba yan siyasar jam’iyah ko kungiyah bane, illah iyaka dai mucewa al’umma suzabi wanda mukaga shiyafi chanchanta,idan zabe yazo mucewa jama’a suzabe shi,ballantana har nayi barazanar fita daga wata jam’iya zuwa wata jam’iyah.

Yakara dacewa” wannan karyace ya kwantaramin,bamu da alaka da wani dan siyasa ko mai mulki indai ba alaka ta addini ba

Yanzu dai sheikh kabiru gombe yabawa muaz magaji dan sarauniya awa goma sha biyu (12) domin yafito yajanye kalamansa ko kuma su makasa kara a gaban kotu.

Malamin yayi alkawarin yiwa muaz magaji hukunci muddin yakasa kawo hujjoji ko kuma yafito yakaryata kansa kafin cikar wannan lokacin (wato awa 12).

0 comments on “WATA SABUWA: Kotu ce Zata Rabani da Muaz magaji – kabiru gombe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *