Kishi : Matashi ya hallaka abokin takararsa adakin budurwar dasuke takara akai
Yan sanda a jihar ogun sun kama wani matashi mai suna,Bisi omoniyi, dan shekara 25 bisa zarginsa da kashe abokin takararsa a dakin budurwar dasuke nema tare.
A rahoton da DAILY TRUST ta ruwaito cewa yan sanda sun sami damar kama mutumin bayan dasuka sami rahoton gaggawa a ofis dinsu dake owode egbado.
- Dalilin da yasa amare basa cin kazar da ango ke kawowa a daren farko
- Wani kare ya mutu har lahira bayan ya shinshini dan kampai
A rahoton da jami’an yan sanda suka samu, an bayyana musu cewa wani matashi ya halaka wani mutum da adda agarin ajilete dake jihar osun.
Kakakin rundunar yan sandan jihar,Abimbola oyeyemi ya tabbatar da faruwar al’amarin.
Yace da farko sunyi kokarin sukai wanda aka sara asibiti, amma bayan sunje likita ya tabbatar musu da cewa tuni rai yayi halinsa.
Oyeyemi yakara dacewa abinciken da jami’an yan sanda suka gudanar, sun gano cewa matashin da aka kashe mai suna, akinyemi wahab, yaziyarci dakin abokiyar lalatarsa mai suna,kafayat sakariyau, domin kwana a dakin tareda ita.
“shima wanda ake zargi da kisan yana neman wannan matar, shima kuma a daren yakawo mata ziyara kamar yanda yasaba domin rage dare, amma sai aka hanashi shiga” inji oyeyemi
“Wannan abunne ya fusatashi inda anan take ya balle kofar yashiga da karfin tsiya,amma kuma sai yasamesu a wani yanayi wanda bazai iya kai zuciyar sa nesaba”.
“Daga nan sai samarin suka fara kokawa a junansu, matashin da ake zargi sai ya dauki adda a dakin ya kafta masa sara, wanda hakan yayi sanadiyyar rasa ransa“
Oyeyemi yaci gaba da cewa Yanzu dai ankai gawar dakin ajiye gawawwaki, yayin da ita kuma matar da ake fadan akanta aka nemeta aka rasa









One Comment