Duniya ina zaki damu : An kama wasu yan biyu maza bisa zargin yiwa yarinya yar shekara 9 fyade.
Rundunar yan sandan jihar enugu ta gurfanar da wasu yan biyu a gabanta domin gudanar da bincike akansu, bisa zargin da ake musu na cewa suna da hannu a yiwa wata yarinya yar shekara 9 fyade.
RIGAR YANCI INTERNATIONAL ta wallafa cewa Ya zuwa yanzu kakakin rundunar yan sandan jihar enugu, ASP Daniel ndukwe, ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na NAN faruwar al’amarin, sannan kuma yasa amika yan biyun masu suna, chima Nnamani dakuma Michael Nnamani zuwa sashin binciken manyan laifuka na (CID) ENUGU, domin gudanar da cikakken bincike.
Shugabar kungiyar mata ta WACOL, farfesa joy ezeilo, tayi kira da agaggauta gurfanar da wandan da ake zargi a kotu da zarar an kama su da laifin domin yimusu hukunci.
Rigar yanci international ta ruwaito cewa ” a ranar 28 ga watan nuwamba 2021, WACOL tasamu rahoto akan cewa wasu samari guda biyu yan biyu sunyiwa wata yarinya mai shekaru 9 fyade a yankin akpawpu dake jihar enugu”
Ana zargin wadanda aka kama da laifin cin zarafin yar uwarsu wacce suke tare da ita ta hanyar yi mata fyade.









One Comment