Friday, 24 September, 2021

Ads Banner

Da dumi -dumi; Apc ta kori Tsohon gwamna da kuma wasu mambobi 40.


A kalla jiga-jigan jam’iyar Apc 41 da daya ak kora daga jam’iyar A jahar ENUGU a ranar lahadi 12/9/2021 sakamakon zarginsu dakarya dokar tsarin cikin gida.

A wani jawabi dayayi da manema labarai shugaban kwamitin riko na jihar,ben nwoye, yace mutanen da abun yashafa sun shigar da kara kan jam’iyar batareda bin hanyoyin magance rikicin cikin gida ba.

Leadership ta ruwaito cewa mambobin sun shigar da kara a babbar kotun dake ABUJA suna nema acire nwoye daga mukaminsa.

Sai dai shugaban yabayyana cewa wadanda aka korar aikinsu yasabawa shashi na 21 (D) sashi na V na kundin tsarin mulkin na APC, inji jaridar vanguard kamar yanda Legit.hausa.ng ta bayyana.

Wadanda aka kora sun hada da.

1) Tsohon gwamnan mulkin soja,group capt joe orji

2) Tsohon kakakin majalissar dokokin jihar, hon eugede odo.

3) Tsohon mataimakin dan takarar Gwamna na jam’iyar,prince chikwado chikunta.

4) gen j.o.j okoloagu, tsohon dan majalisar wakilai.

5) chukuemeka ujam, da sauran kuma wasu mambobin 36 kamar yanda Legit hausa ta ruwaito.

0 comments on “Da dumi -dumi; Apc ta kori Tsohon gwamna da kuma wasu mambobi 40.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *