Labaran Duniya

Daga karshe amaryar da angonta yayi mata saki daya a daren farko ta tare da igiya biyu bayan zaman sulhu.

A shekaran jiya ne wani bakano ya rattabawa amaryarsa saki daya bayan kawayenta sun kekashe kasa sai anbasu naira dubu dari biyu (200,000) kafin su bude dakin amarya subar ango yashigo.

KARANTA : Abun takaici : Tsoho mai shekaru 70 yayiwa yarinya yar shekara 7 fyade.

Wannan ce tasa abokan ango sukayi musu tayi akan cewa zasu basu naira dubu talatin (30,000), amma suka kekashe kasa sukace bazasu karba ba.

Wannan daliline yasa angon yakira amaryartasa sau biyu amma taku daga waya,wannan ce tasa angon ya fusata ya makawa abar kaunar tasa saki 1 ta hanyar turamata da text message.

KARANTA : Kishi : Budurwa ta cakawa saurayinta wuka bayan ta duba whatsapp dinsa.

Sai dai yanzu haka bayan an zauna anyi sulhu, manya sun shiga tsakani, ansamu daidaituwa, ango yamayarda amaryarsa, inda yanzu haka amaryar ta tare da igiya biyu.

Sai dai muce allah ya kiyaye gaba.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button