Labaran Duniya

Da gaske za a kulle maka whatsapp idan baka turawa mutane sakon murya ba.

Mutane da dama sun fito suna ta tofa albarkacin bakinsu a game da wannan batu da aketa yadawa musamman ma a dandalin sadarwa na WhatsApp.

Sakon mai minti 3-4 yana bayyana a muryoyi da yaruka daban-daban,wani a yaren hausa, wani turanci da dai sauransu.

A wata hira da yayi da gidan Radion freedom radio, Aliyu dahiru aliyu, ya bayyana wannan sako da ake turowa a matsayin sakon karya kuma na yaudara.

Sannan kuma a wani bincike da mukayi kuma muka tabbatar da binciken, mun gano cewa wannan maganar bata da tushe.

Ma’ana dai ba kamfanin whatsapp bane suke aiko da wannan sako, wani mutum ne yazauna ya kirkireshi domin cimma wata manufa tasa.

Har yanzu ba’a gano abunda mai wannan sako yake nufi ba ko kuma yakeson cimma ba, amma dai ansan cewa wannan sakon karyane acikinsa.


KARIN WASU LABARAN

  • “Kwankwasiyya ce muke” sabuwar wakar kosan waka mai zafi.
    Shahararren mawakin kwankwasiyya, wanda yake jihar katsina, kosan waka, yasaki sabuwar wakar jagoran tafiyar siyasar kwankwasiyya na duniya, engr dr rabi’u musa kwankwaso. Tun a kwanakin baya mawakin yayi magana akan sakin sabuwar wakar tasa wacce tazo da sabon salo. Ga videon wakar nan akasa ku more kallo kyauta. Sabuwar wakar kosan waka “kwankwasiyya ce …

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button