Kannywood

Ana amfani da mata kafin sakasu a Film: Nafisa Abdullahi tayiwa Naziru Sarkin waka zazzafan martani

Ana amfani da mata kafin sakasu a Film: Nafisa Abdullahi tayiwa Naziru Sarkin waka zazzafan martani

Bayan wani bidiyo da Naziru Sarkin waka ya yi domin bude gaskiyar abinda aka dade ana boyewa da ya shafi matsalar sallamar jarumai kuɗin aikinsu da kuma batun da ya yi na cewa ana neman wasu matan kafin a saka su a Film.

Wannan batun ba karamin tayarwa da jaruman kannywood hankali ya yi ba, inda aka samu dayawa daga cikin su na maida masa martani kala daban-daban. A yanzu haka ma dai Nafisa Abdullahi ta yi nata martanin inda ta yi kira ga Naziru Sarkin waka da ya ambaci sunan wadanda ya san sun aikata laifin da ya ambata ba wai ya yiwa masana’antar kannywood kuɗin goro ba.

Nafisa Abdullahi ta fara da cewa tun farko bata yi niyyar sanya kanta cikin rikicin da bai shafeta ba, sai dai kuma tana ganin wannan batun da Naziru ya kawo abu ne mai bukatar dubawa saboda dole ya shafi duk wata mace da ke masana’antar kannywood.

Nafisa ta yi kira ga Naziru da ya fito ya ambaci sunan duk wasu da ya sani suna aikata wannan laifin da ya ke ikirarin ana aikatawa ko kuma ya gabatar da hujjojinsa domin hakan ne zai sa wadanda abun bai shafesu ba su samu damar kubuta daga dukkan zargi. Ina kuma ba haka ba, to zai fi kyau kafin ya furta magana da ta kasance ta zargi to ya samu hujja.

Nafisa Abdullahi dai ta kara da yin kira ga sauran jarumai mata da ke cikin wannan masana’anta da duk wadda ta san an taba neman ta da lalata domin a sanyaya a film to ta fito ta yi bayani domin su za su tsaya mata wajen ganin an ƙwato mata hakkin ta.

Wannan batun na Nafisa Abdullahi ta rufe shi da cewa kasar Nigeriya da ma masana’antar kannywood na da dokoki kuma babu wata doka da ta bada dama ga producer ko director da ya nemi mace da lalata kafin ya sanyata a Film. Saboda haka dukkan. Wanda aka kama da aikata hakan sai an hukunta shi.

Daga karshe Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa mutane da dama a wannan masana’antar tasu na da sana’o’in da su ka rike ba wai kawai sun dogara da Film ba ne, amma idan ma an samu wanda su ka dogara da Film ɗin to wannan ra’ayin su ne.

Ana amfani da mata kafin sakasu a Film: Nafisa Abdullahi tayiwa Naziru Sarkin waka zazzafan martani
Ana amfani da mata kafin sakasu a Film: Nafisa Abdullahi tayiwa Naziru Sarkin waka zazzafan martani

Yawan jaruman kannywood ɗin da suka yiwa Naziru Sarkin Waka martani.

Bayan hirar da BBC Hausa ta yi da ladin chima an samu wasu daga cikin jaruman kannywood da su ka yi martani kan batun biyanta dubu biyu a matsayin kuɗin aikinta. Martanin jaruman baki daya ya karkata ne kan cewa tsohuwar bata yi musu adalci ba, domin ana yi mata sallama mai kyau sabanin abinda ya bayyanawa yan jaridu.

Amma tun daga lokacin da Naziru M Ahmad ya fito ya goyi bayanta tare da fasa wani kwan da ba a ma san da shi ba na batun neman yan mata da iskanci kafin a saka su a Film, sai lamarin ya canza alkibla inda aka yi caa kan sa tare da neman ya gabatar da shaidu sa na abinda ya fada indai gaskiya ne.

Karanta>> Madagwal: ana lalata da mata kafin a saka su a Film a kannywood

A cikin jerin jaruman da su ka yiwa Naziru Sarkin Waka martani akwai

  • Ali Nuhu
  • Falaki A Dogaro
  • Bello Muhammad Bello BMB
  • Nuhu Abdullahi
  • Aminu S Bono
  • Rashida Abdullahi Mai Sa’a
  • Rukayya Dawayya
  • Nafisa Abdullahi

Da sauransu. Wanann jerin sunayen jaruman da muka lissafi ba iya su ne kawai su ka maida martani da wannan jarumi ba, domin suna nan da yawansu.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button