An yankewa Malami hukuncin Daurin Rai da rai a gidan kaso bisa laifin yiwa yarinya yar shekara 5 fyade.
Wata babbar kotu dake zamanta a garin kazaure dake jihar jigawa, ta samu wani malami mai suna, mista Makasusi sunusi, Da laifin lalata yarinya yar shekara 5 ta hanyar yima ta fyade, inda aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
Wacce ta jagoranci shari’ar Mai shari’a,Hussaina adam aliyu, ta samu sunusi da laifin lalata da wacce aka azabtar,(ansakaya sunanta) wacce dalibace a makarantarsa a ranar 4 gawatan February na shekarar 2021, wanda hakan yasabawa dokar panel code na jihar jigawa na 2014, kamar yanda RIGAR YANCI INTERNATIONAL ta ruwaito.
Wanda ake zargin ance yayiwa dalibar fyadene acikin makarantar dayake koyarwa a garin kazaure na jihar jigawa, daga bisani aka kamashi aka gurfanar dashi a gaban kotu bisa zargin laifin fyade.
Mai shari’a hussaina adamu, ta bayyana cewa masu gabatar dakara sunyi nasarar tabbatar da hujjoji batareda wata shakka ba, wannan ce tasa mai shari’ar ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai kamar yanda sashe na 3 na kundin laifuffuka na jihar jigawa na shekarar 2014 yatanada.
A WANI RAHOTON KUMA
Rundunar yan sanda a jihar jigawa, ta tabbatar da kama mutane biyu tareda tsaresu bisa zargin yiwa kananan yara fyade.
A wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan yafitar, ASP lawan shisu Adam, ya bayyana cewa yanzu haka ana nan ana tuhumar Hussaini yahaya mai shekaru 15, dakuma dabo abubakar mai shekaru 50, bisa zargin yin lalata da yara yan shekara 9 a wurare biyu daban-daban.
KARANTA: Ankama wani saurayi Dayake yaudarar Yan mata yana guduwa da wayoyinsu.
Kungiyar RIGAR YANCI INTERNATIONAL ta bayyana cewa, ana zargin yahaya abubakar da aikata ta’asar sa a garin kwalam dake karamar hukumar taura, shikuma Dabo Abubakar yayi tasa a kauyen unguwar gamji dake karamar hukumar gwiwa ta jihar.
Zaku iya ajiye mana comments a akwatin sako dake kasa domin bayyana ra’ayoyinku.








