Yanda mahaifina da kakana suka dinga lalata dani har na tsawon shekara biyu-inji wata yarinya mai shekaru 13.
Rahotanni dasuke fitowa daga jihar osun, sun bayyana cewa hukumar NSCDC ta kama mahaifi dakuma kakan wata yarinya dasuka yiwa yarrasu mai shekaru 13 fyade.
Mai magana dayawun shugaban hukumar ta jihar,mr Adigun Daniel ne yasanar da hakan a ranar litinin ga manema labarai,ya bayyana cewa tun ranar juma’a da yarinyar tayi korafi aka kama wadanda ake zargin.
KARANTA :Yan sanda sun gano gawar namiji da mace a mota a jihar kano.
MUJALLAR IDON MIKIYA ta bayyana cewa, wata makwafciyarsu yarinyarce takai korafi wajen jami’an tsaro,bayan kuma da aka binciki yarinyar itama sai ta tabbatar da haka,tareda cewa iyayen nata sun kwashe kusan shekaru 2 suna lalata da ita.
Nan bada jimawa ba zamu kawo muku cikakken rahoton.
KARANTA : Duniya ina zaki damu : Dan shekara 34 yayiwa diyar Abokinsa mai shekaru 10 fyade.









3 Comments