Innalillahi wa’inna ilahi raji’un! An tsinci gawar wata mata a daddatse acikin buhu.
A garin kano, al’ummar garin gurin gawa dake karamar hukumar kumbotso a jihar kano,sun tashi cikin gagarumin rashin hankali bayan da aka tsinci gawar wata mata an daddatsata ansaka acikin buhu an jefar da ita a wani kango.
A rahoton da jaridar DAILY NIGERIAN ta fitar ya bayyana cewa, mutanen garin sun fadi cewa yarane suka gano gawar matar alokacin da suke wasan buya.
- Dalilin da yasa amare basa cin kazar da ango ke kawowa a daren farko
- Wani kare ya mutu har lahira bayan ya shinshini dan kampai
Yaran suna cikin wasan buya sai sukaga jini yana kwaranyowa daga cikin kangon, hakan ce tasa yaran sukashiga domin suga menene yake zubar da jini aciki,suna shiga sai sukaga ashe jinin daga cikin wani buhu yake kwaranyowa, a firgice yaran suka fita domin suje sugayawa manyan garin inji rahoton da mazauna kauyan suka bayar.
Bayan da manya sukazo, har da mai unguwar yankin, alhaji ghali sulaiman,sai sukaga cewa ashe jikin macece an daddatsa, lamarin dayasa suka kasa gane ko wacece kenan.
Wata mata a garin wacce ta naimi asakaya sunanta ta bayyana cewa, wannan karon bashi ne na farko ba da hakan tafaru,tace abayama andan samu irin wannan matsalar.
Matar takara dacewa, shikansa kangon matattarar batagari ne, dakuma sharane a jibge.
A nashi bangaren mai unguwa sulaiman, yayi kira da al’umma akan su kwantar da hankalinsu, inda yakara dacewa ansanar da hukumomi halin da ake ciki.
Kakakin rundunar yan sandan jihar kano, ABDULLAHI HARUNA KIYAWA, ya tabbatsr da faruwar al’amarin, inda yace tuni jami’an bincike na rundunar suka fara gudanar da aiki domin kama batagarin dasuka aikata wannan ta’asa.
Mun dakko muku wannan rahoto dag jaridar DAILY NIGERIAN , su suke da hakkin mallaka akan wannan rubutu da muka dora.








