Labaran Duniya

Kotu ta yankewa mutumin daya kashe matarsa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Wata babbar kotu a jihar kano ta yankewa wani mutum mai suna,Aminu inuwa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kamashi da laifin kisan matarsa

A wani rahoto da jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito ya bayyana cewa mutumin yakashe matar tasa mai suna safara’u usman a shekarar 2019.

Aminu wanda kotu bata bayyana asalin shekarun saba, mazaunin unguwar gwazaye ne dake gwale a jihar kano.

Mai shari’a,usman na abba, ya tabbatar da cewa masu shigar da kara sun gabatar da gamsassun hujjoji a game da karar dasuka shigar.

Lauyan mai gabatar da kara,lamido soron dinki, ya bayyanawa kotu cewa, mutumin ya chaka wa matar tasa wuka a makogaro lokacin da wata sa’insa ta hadasu, wanda hakan yayi sanadiyyar rasuwarta nan take.

Yacigaba da cewa, bayan mutumin ya kasheta, sai yasamu kangon daki a gidansa ya binneta aciki.

Lauyan ya gabatarwa da kotu shaidu guda uku da kuma hujjoji guda shida domin tabbatar da abunda yake fada,kamar yanda labarai 24 ta ruwaito.

Sai dai kuma wanda ake zargi ya musanta hakan, yayinda lauyansa yakasa kareshi daga tuhumar da ake masa da gamsassun hujjoji.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button