Kannywood

Tohfa : Yan Hisbah sun kama Fati Washa A gidan Gala Na jihar Jigawa sannan annemi sadiya haruna an rasa.

Rahotannin Dasuke fitowa daga jihar jigawa,sun tabbatar da cewa,hukumar hisba reshen jihar sun yi ram da Jarumar finafinan hausa masana’antar kannywood,Fati Washa A gidan gala dake jihar ta jihawa.

Gidan Watsa labarai na AMINTACCIYYA NEWS sun tabbatar da faruwar al’amarin,inda suka bayyana cewa, Yin rawar gala a kaf fadin jihar yasabawa dokar jihar, sannan kuma yasabawa dokokin hukumar ta hisba.

Yan Hisbah sun kama Fati Washa A gidan Gala Na jihar Jigawa. Jarumar kannywood
Jaruma fati washa

Hukumar yan hisban ta kara dacewa”Dan haka duk wanda ya karya doka yayi,to za’a kamashi,sannan kuma za’ayi masa hukunci dai-dai da abunda ya aikata”.

yanzu haka dai ana nan ana ta dakon jiran ganin hukuncin da hukumar zata yankewa jarumar ta kannywood.

A WANI RAHOTO KUMA : Har yanzu ba’aga sayyada sadiya haruna ba.Danginta suna zargin Jai’an tsaro da tsare musu yar uwa.

Dangin sayyada sadiya haruna sun kara fitowa da bayyana kokensu a game da rashin bayyanar yarsu da kuma rashin sanin ainihin inda take.

Sanarwar hakan Tafito acikin wani bidiyo da daya daga cikin Yaran Sayyada yafitar,yana mai sanar da al’umma da kuma jami’an tsaro cewa su taimaka idan sayyada tana hannunsu su gayamusu ko kuma su kira lambar waya suyi musu karin haske.

Yanzu haka dai ana can a shafin Jarumar na Instagram ana jimamin rashinta,yayin da wasu suka jingina batan nata da kamun yansanda,inda suke ta cewa jarumar tana hannun yan sanda ne,wasu kuma suke tambayar sunan fim din,ma’ana basu yarda da abunda akace ya faru da sayyada ba.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button