Labaran Duniya

Subhanallahi : Wani matashi ya rataye kansa a kano.

Wani matashi mai kimanin shekaru 30 da ba’a bayyana sunansa ba yarataye kansa a karamar hukumar kiru, dake jihar kano a ranar talatar data gabata.

Matashin yarataye kansane a bishiya dake gonar wani mutumi, daga baya mai gonar ya ganshi inda nan take ya garzaya yasanar da hukumar yan sanda.

Daga bisani jami’an yansanda suka iso gurin,suka sauko dashi sannan suka garzaya asibitin murtala dashi,a can likitoci suka dubashi sannan suka tabbatar musu da ya mutu.

Rundunar yan sanda jibar kano sun tabbatar da faruwar al’amarin tabakin jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan,DSP Abdullahi haruna kiyawa, kamar yanda wani rahoto da mujallar dimokuradiyya tafitar ya bayyana.

Kiyawa yace har yazuwa yanzu bincike suke basu gano musabbabin rataye kan nashi ba,kuma ya tabbatar dacewa haryanzu gawar marigayin na asibiti,yan’uwansa basuje sun dauki gawar ba.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button