Kannywood

Hotuna da kuma videon daurin auren jaruma maryam waziri( laila labarina).

A rahotannin dasuka fito daga majiya mai tushe, ta tabbata cewa jaruma maryam waziri, wacce akafi sani da laila acikin shirin labarina tayi aure a yau ranar juma’a 26/11/2021.

A wani video wanda jarumar ta wallafa acikin story a shafinta na Instagram, yanuno jarumar zaune cikin kwalliya tana murmushi da dariya, yayin da videon yafito da wata waka mai taken” lale amarya lale ango”.zamu saka muku videon akasan wannan rubutun.

Aminu saira, director na shirin labarina series wanda jarumar take haskawa, ya tabbatar da faruwar al’amarin ta hanyar wallafawa a shafinsa na Instagram tareda rubutu na taya jarumar murna.

https://www.instagram.com/tv/CWwPat_K-Md/?utm_medium=copy_link

Wannan shine rubutun taya murnar daurin auren jarumar wanda aminu saira yayi mata, sannan kuma aminu saira yace sunyi missing din jarumar, wanda hakan ke nuni da cewa ba lallai taci gaba da haska ahirin labarina ba.

Sannan kuma tsayayyen account din masana’antar kannywood shima ya tabbatar da auren yayinda shima ya taya jarumar murnar aurenta.

Hoto:kannywood Instagram account

Yanzu dai sai muzuba ido domin ganin shin ko jarumar zata cigaba da fitowa a fina-finai ko kuma aure zai boyeta?.

Ga videon da mukayi muku alkawarin saka muku na daurin auren jarumar 👇👇.

Bidiyon amarya maryam waziri. Video daga aminu saira.

Muna mata allah yasanya alkhairi yabasu zaman lafiya.

Kuyi comments domin kuyi mata fatan allah yasanya alkhairi 👇👇

Read Also

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button