Labaran Duniya

Dan shekara 71 ya mutu yayin da yake tarawa da karuwa.

Wani magidanci yayi numfashinsa na karshe yayin da yake tsakar jima’i da karuwa.

Lamarin yafaru a kauyen ogijo karamar hukumar shagamu jihar osun dake kudu maso yammacin najeriya.

Mutumin da aka bayyana sunansa da ajibola olufemi mai kimanin shekaru 71, bayanai sun nuna yaje otal dinne domin ya huta, anan ne yahadu da wata karuwa yar gidan magajiya, inda sukaje suka fara lalata,suna tsaka da tarawa sai yafado matacce,inda anan take yayi numfashinsa na karshe, inji wata ma’aikaciyar otal din wacce ta naimi asakaya sunanta.

Bayan ansanar da yan sanda abunda yafaru, sai suka dauke gawar aka tafi da ita dakin ajiye gawa na garin shagamu,sannan akayiwa iyalan mutumin magana aka sanar dasu abinda yafaru.

Bayan tafiya da gawarsa,Jami’an tsaro sunyi caraf da karuwar domin fadada bincike a kan abunda yayi sanadin rasuwar mutumin.

Kakakin rundunar yan sandan jihar,ogin abimbola oyeyemi, ya tabbatar da faruwar al’amarin, yace suna kan bincike domin gano musabbabin faruwar al’amarin.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button