Labaran Duniya

Bacin rana : Dan tauri ya fafake cikinsa a lokacin dayake yanka wuka a yayin bikin tauri.

Wani dan tauri a jihar kano mai suna nadabo alhassan mai kimanin shekaru 40, ya hadu da tsautsayi a wurin aikinsa na tauri, a karamar hukumar sumaila a jihar kano.

Jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA ta ruwaito cewa, lamarin yafarune a lokacin da alhassan yafito yayi kirari yayi kirari, sai ko yafara dabawa kansa wuka ta ko ina a sassan jikinsa.

KARANTA : Wata Sabuwa : bidiyo akan yanda Matan Wani Mutum Suka rabu dashi Saboda yaki ya daina sata.

Jaridar ta ruwaito cewa, a lokacin da alhassan ya rufe idonsa ya zage yana ta gabzawa kansa karfe, sai abokanansa na aiki suka fara yimasa magana suna cewa ” ta isa haka” amma ina, tsuminsa na tauri yariga ya tashi, kawai sai ganin tumbinsa akayi a waje.

Ai kuwa kafin kace kwabo, alhassan yafadi cikin jini shame-shame,nan da nan aka kira yan sanda sukazo suka tafi dashi asibiti.

Kakakin rundunar yan sandan jihar kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda yace tuni kwamishinan yan sandan jihar kano, Sama’ila Shuaibu dikko yabada umarnin garzayawa da dan taurin asibiti.

To amma acewar jaridar ta DAILY NIGERIAN HAUSA, duk wannan abun alhassan ya tsallake rijiya da baya, inda kakakin rundunar yan samdan jihar kano ya tabbatar da cewa yanzu haka alhassan yana nan yana karbar magani a asibitin gani dake Sumaila.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button