Labaran Duniya

Yan sanda sun gano gawar namiji da mace a mota a jihar kano.

Rundunar yan sanda a jihar kano, tace ta gano gawar mutum biyu, mace da namiji acikin wata mota kirar siyana akan hanyar zuwa katsina daga jihar.

 

A sanarwar da kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP abdullahi haruna kiyawa yafitar jiya alhamis, rundunar tace tagano mamatan, wanda ya bayyana sunansu da steven ayika dakuma chiamaka Emmanuel,dukkansu su biyun yan unguwar jaba ne, dake karamar hukumar fagge a jihar kano, kuma dukka su biyun suna kwance a bayan motar.

DAILY NIGERIAN HAUSA ta bayyana cewa, kiyawa yakara dacewa,rundunar takarbi rahoton cewa anga wasu mutane biyu a kwance abayan mota dukansu basa motsi,imda tuni jami’anta suka garzaya gurin.

Kiyawa yace” a ranar 23 gawatan November da misalin karfe 4:40 na safe, mjn samu rahoton cewa, anga wata mota dake kan hanyar kano zuwa katsina dauke da mutane biyu aciki, namiji da mace amma kuma suka su biyun basa motsi”.

 

 

 

“Bayan samun rahoton kwamkahinan yan sandan jihar kano, CP sama’ila shuaibu dikko, ya umarci tawagar yan sanda bangaren bincike dasu garzaya gurin da lamarin yafaru.

“Nan take tawagar ta garzaya inda al’amarin yafaru, bayan sun isa sai aka kwashe gawawwakin,inda aka garzaya dasu asibitin kwararru na murtala Muhammed,a nanne likitoci suka tabbatar da sun rasu”.

“Yanzu haka dai muna cikin bincike” inji Dsp abdullahi haruna kiyawa.

 

Duniya ina zaki damu : mahaifi yayi yunkurin sayar da yayansa mata guda biyu akan kudi naira 700,000.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button