Wata sabuwa : Ancafke maiyiwa yan luwadi wayo yana Damfararsu kudi a kaduna.
 Ancafke maiyiwa yan luwadi wayo yana Damfararsu kudi a kaduna,
Matashin mai suna, Abdulrahman Danagana, ankamashi ne Da laifin yiwa yan luwadi wayo yana damfarar su kudi a jihar kaduna dake arewacin najeriya.
Mutumin da ba’a bayyana shekarunsa ba ana zarginsa da bude shafi a wani group na masu aikata luwadi, inda acikin group din yake hira dasu ya nuna musu cewa ya yarda su aikata luwadi dashi.
KARANTA : Abun takaici : Tsoho mai shekaru 70 yayiwa yarinya yar shekara 7 fyade.
Bayan sunyi yarjejeniya sai yace su aika masa hotunansu tsirara, idan suka aika masa sai yayi musu barazanar cewa ko su bashi kudi ko kuma yaturawa duniya kowa yagani.
KARANTA : Barayin waya a kano sun hallaka wani matashi mai shekaru 30 a kano.
Matashin yayi amfani da sunayen karya da dama a ahafin, inda aka kiyasta cewa ya damfari yan luwadin kudade kimanin $8420 kwatankwacin naira 3,466,598.20 a kudin najeriya.
Yanzu haka dai angurfanar da matashin a gaban kotu, inda alkali ya daga karar zuwa 12 gawata,sannan kuma an bayar da belinsa akan kudi naira miliyan 1 da wanda zai tsaya masa, a rahoton da jaridar IDON MIKIYA TA FITAR








