Labaran Duniya

Dalibar BUK Da aka sace jiya ta bulla a sabon gari

A jiya laraba labarin sace dalibar makarantar BUK mai suna, sakina bello a hanyar ta takomawa gida a daidai rijiyar zaki yakarade shafukan sada zumunta musamman dandalin Facebook.

Sai dai kuma a yau alhamis ne aka ga Dalibar A unguwar sabon gari dake yankin fagge a jihar kano.

Dalibar dai ta bayyana cewa ta kubuto ne daga hannun wadanda sukayi garkuwa da ita.

Dalibar tayi amfani da wayar salula ta kira da’uwanta, inda ta bayyana masa cewa ta kubuto daga hannun wandanda suka sace.

Tun da farko dai mutanen dasuka saceta sun bukaci a biyasu miliyan 100 a matsayin kudin fansar ta.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button