Uncategorized

Yan sanda sun cafke wata mata mai kaiwa yan bindiga man fetur a jihar katsina.

Rundunar yan sandan jihar katsina ta cafke wata mata mai kaiwa yan bindiga man fetur.

A ranar 14 September 2021 ne yan sandan suka cafketa yayin dasuke sintiri akan titin kofar buga zuwa jibiya, suka kama matashiyar Mai suna,Rashida ussaini mai shekaru ashirin da biyar.

Ta baiyanawa hukumar yansandan cewa ita yar karamar hukumar kankarace amma daga baya ta canza baki tace ita yar jahar gombe ce, yanzu kuma ta sake cewa ita yar kauyen yarji ce dake a jamhuriyar nijar kamar yanda dan sandan dake karanta bayani ya bayyana acikin videon da jaridar Legit.hausa.ng ta wallafa.

Dan sandan yace Lokacin da aka chafketa ankamata kayayyaki dasuka hada da, buhu dauke da jarkoki uku na man fetur da kuma babbar leda cike da man fetur wanda shima zai kai kimanin jarka uku.

Dan sandan ya bayyana cewa Matar ta kasa kare kanta a gaban hukumar ta yansanda,saboda a cewarta zataje kauyen yarji ne,amma kuma kowa yasan abunda ke faruwa na hana sayarda man fetur a jahar ta katsina.

Yakara dacewa bayan sun gama bincike zasu gurfanar da matar a gaban kotu bisa tuhumarta da laifuka kamar haka.

1) karya umarnin gwamnan jihar katsina.

2) sa hannu a ayyukan ta’addanci da yan ta’adda keyi.

Mun dakko muku wannan rahoton daga videon da jaridar legit hausa ta wallafa a shafinta na youtube, ga masu bukatar su kalli videon zaku iya danna Videon matar da yansanda suka kama tana kaiwa yan ta’adda fetur domin ku kalla.

Read Also

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button