Labaran DuniyaUncategorized

Wani mutum yayiwa diyarsa ta cikinsa yar shekara 19 ciki bayan yasaki mahaifiyarta.

Wani abun kunya kuma abun kyama daya faru a jihar osun dake kudancin najeriya yajawo hankulan al’umma da dama, musamman ma akafafen sada zumunta, inda al’umma keta allah wadai da abunda yafaru.

Rundunar yansandan jihar osun ta kama wani mutum mai shekaru 45 bisa zarginsa da dirkawa yar cikinsa ciki kamar yanda jaridar Vanguard ta ruwaito.

An cafke Mutumin mai suna, olaoluwa jimoh, dake zaune a yankin ode remo,biyo bayan karar da diyar tasa takai ofishin yansanda.

Budurwar ta shaidawa yan sandan cewa, mahaifinta yayi lalata da ita lokuta da dama, kuma yayi mata barazanar kisa matukar ta tona masa asiri.

Yarinyar takara dacewa mahaifiyarta da mahaifinta sun rabu shekaru da dama dasuka wuce.

Daga karshe dai mutumin ya amsa laifinsa, amma kuma yace sharrin shaidanne.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button