Siyasar kano : Ganduje yataya kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Gwamnan kano, Dr abdullahi umar ganduje yataya tsohon gwamnan kano,sanata, engr dr rabiu musa kwankwaso, murnar zagayowar ranar haihuwarsa da yake gabatarwa yau.
A wani hoto da Sarkin yakin kwankwasiyya yafitar,salisu yahaya hotoro,wanda jaridar daily trust ta ruwaito,ya bayyana sakon da gwamnan yafitar.
Acikin sakon gwamnan ya bayyana cewa amadadinsa shida iyalansa dama daukacin jam’ar kano, yana mai taya sanata rabiu musa kwankwaso murnar zagayowar raran haihuwarsa.
“Ni dr abdullahi umar ganduje, zababben gwamnan kano,a madadin iyalaina da kuma daukacin al’ummar jihar kano, ina taya tsohon gwamnan jihar kano, engr dr rabiu musa kwankwaso murnar cika shekaru 65” injishi.
- Dalilin da yasa amare basa cin kazar da ango ke kawowa a daren farko
- Wani kare ya mutu har lahira bayan ya shinshini dan kampai
- Rahma Sadau: Yadda na tsallake rijiya da baya a harin jirgin kasar kaduna
Yacigaba dacewa “dukkanin godiya ta tabbata da allah madaukacin sarki daya bamu ikon ganin wannan rana ta zagayowar haihuwarka”.
Ya bayyana cewa tabbas sun tabbatar da irin ayyukan da sanata kwankwaso yayi a lokacin da yana gwamna shikuma ganduje yana mataimaki,sannan ya roki kwankwaso akan yacigaba da taimakon kano da kanawa da irin ayyuka da kuma hazaka da tunaninsa a matsayinsa na tsohon minista kuma sanata.
Daga karshe yace ya bi bayan miliyoyin al’ummar jihar kano dama duniya baki daya gurin taya kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa, yana masa fatan allah yakara lafiya da kuma farincik a rayuwa.



One Comment