Labaran Duniya

Innalillahi! Makocinmu yace na’ara masa wayata zai kalli labarina, daga zuwa kaimasa sai yayi min fyade.

Iyaye dan allah acigaba da saka idanu akan yan’uwanmu mata musamman domin sanin da irin abokai ko kuma kawayen dasuke mu’alama, wani lokacin bawai rashin tarbiyyar yaro bace kawai take kaishi kwadayi, har da sakacin iyaye,dan allah acigaba da kula.

Anan kuma mun kawo muku videon wata budurwa wacce ta bayyana yanda akayi mata fyade daga cewa tabada aron waya, wanda zata arawa wayar makocinsu ne wanda suke gidan haya daya mai suna shamsu.

Acikin videon wanda yake kasan rubutunnan Budurwar maisuna amina musa ta bayyana sunan cewa suna wasa da dariya da saurayin wanda yayi mata fyaden mai suna Shamsu, domin a gidan haya daya suke tare, idan yashigo gida yana tambayar tana ina har sun saba sosai.

Ta bayyana cewa a ranar da abun yafaru tana daki sai taji shamsu yana kwallamata kira, bayan tazo sai yake tambayar ta ko tanada chaji a waya tabashi ya kalli labarina, sai tace masa 50 fasent gareta amma zata bashi ya kalla kadan.

Bayan tabashi wayar, zatafita kenan sai taji ya fisgota hannunta, hakan yasa tajuyo tana tambayarshi menene haka, kafin tagama rufe baki sai yayi kiss dinta tareda dura mata wani abu abaki, anan take hankalinta ya gushe.

Budurwar tacigaba da bayyanawa RIGAR YANCI INTERNATIONAL cewa, daganan hankalinta yagushe batasan maiyafaru ba, sai dai kawai tashi tayi taji shamsu yana cewa idan tafito tarufe musu daki.

Matar yanzu haka dai takai kokenta zuwa RIGAR YANCI INTERNATIONAL, kungiyar dake kare hakkin wanda aka zalunta ko kuma wadanda suka kawo karar wani dan jarida ko dan siyasa akan yiwa al’umma almundahana.

Ga dai cikakken videon yanda al’amarin yafaru daga bakin matar ku kalla a kasa, ku danna wannan videon dake kasa domin ku kalla.

Zaku iya bayyana mana ra’ayoyinku acikin akwatin comments akan wannan al’amari daya faru, wakuke ganin yana da laifi aciki ? Sakacin budurwar ne ko na iyayenta?

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button