Duniya ina zaki damu : mahaifi yayi yunkurin sayar da yayansa mata guda biyu akan kudi naira 700,000.
Rundunar yan sandan civil defence a jihar akwa ibom, tace tasamu nasarar kama wani mahaifi wanda yake yunkurin sayarda yayansa mata guda 2 akan kudi naira dubu 700.
Kakakin rundunar ,ukeme umana, shiya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar a birnin uyo ranar laraba.
Rahoton DAILY NIGERIAN HAUSA, ya bayyana cewa, an cafke mai laifin a wani asibiti mai suna full care dake kan titin ekpenya a jihar uyo, bayan wani mai gadi ya tseguntawa rundunar yan sandan.
KARANTA : Yanda Yayana da mijin yayata dakuma kuma yayan mijin yayata su uku sukayi min fyade.
Umana yace an cafke mahaifin ranar 15 ga watan November da misalin karfe 1:15 tare da yayan nasa, abasifreke edet mai shekaru shida dakuma rachael edet mai shekaru hudu.
Kakain yakara dacewa bayan mahaifin yashiga hannu, yafadawa jami’an tsaro cewa, shi yana zaune ne a didikim dake kasar kamaru.
“Yakuma bayyana mana cewa wai talauchi ne da matsin rayuwa sukasa shida matarsa dake can adidikim din suka yanke shawarar siyarda yayan nasu” inji umana.
Umana yakara dacewa yanzu haka angama binciken farko,inda rundunar zata mayarda maganar zuwa hukumar yaki da fataucin dan adam domin kaishi kotu.
MAJIYA DAGA : DAILY NIGERIAN HAUSA









2 Comments